Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta ce Kotun Ɗaukaka Ƙara ta sake tabbatar da halaccin shugabancinta na ƙasa, bayan ta yi watsi da ƙarar da wasu mambobin Kwamitin Amintattu na jam’iyyar (BoT) suka shigar.
A cikin sanarwar manema labarai mai kwanan wata 4 ga Nuwamba, 2026, mai ɗauke da sa hannun Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na Jamiyyar, Jungudo Haruna Mohammed, ta bayyana hukuncin a matsayin nasara ga tsarin mulki, halastaccen shugabanci da haɗin kan jam’iyyar.
PDP ta ce kotun ta tabbatar da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke a baya, inda ta yi watsi da ƙarar da ake zargin Sanata Adolphus Wabara da Farfesa Jerry Gana, tare da Babangida Mu’azu Aliyu, Maryam Inna Ciroma da wasu suka shigar.
Jam’iyyar ta bayyana cewa waɗanda suka shigar da ƙarar suna aiki ne ƙarƙashin wani Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa na Riƙo (Interim National Working Committee), wanda take zargin ba bisa ƙa’ida ba ne, ƙarƙashin jagorancin Kabiru Tanimu Turaki, SAN.
PDP ta ce Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta yanke hukuncin ne baki ɗaya, tare da tabbatar da hukuncin ƙaramar kotu da kuma umartar waɗanda suka shigar da ƙarar da su biya ƙarin kuɗaɗen shari’a.
Sanarwar ta ce: “Wannan hukunci babbar nasara ce ga PDP, bin doka da oda, da kuma fifikon kundin tsarin mulkin jam’iyyar.”
Jam’iyyar ta ƙara da cewa hukuncin ya tabbatar da halaccin shugabancin Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC), ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abdulrahman Mohammed a matsayin Shugaban Jam’iyya na Ƙasa, da Sanata Samuel N. Anyanwu a matsayin Sakataren Jam’iyya na Ƙasa.
Ta kuma bayyana cewa hukuncin ya kamata ya kawo ƙarshen duk wani shakku game da sahihancin shugabancin jam’iyyar, tare da zama gargaɗi cewa dole ne a gudanar da harkokinta bisa kundin tsarin mulki da ƙa’idojinta.
PDP ta yi kira ga mambobinta, shugabanni da masu ruwa da tsaki da su mutunta hukuncin kotun, su haɗa kai, su kuma mayar da hankali wajen sake gina jam’iyyar da shirye-shiryen tunkarar zaɓe da sauran ayyukan siyasa.
Sanarwar ta ce: “Hakkinmu ne na bai ɗaya mu kare jam’iyyar, dawo da haɗin kan ta, tare da sake sanya ta a matsayin sahihiyar madadin siyasa ga ’yan Najeriya.”
