Babban alkalin kotun tarayya ya sauya alkalin da zai saurari karar da tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar ADC na kasa, Nafiu Bala Gombe, ya shigar yana kalubalantar shugabancin jam’iyyar karkashin jagorancin Sanata David Mark.
Jaridar TheCable ta rawaito, an mayar da karar ga Alkalin Kotun Tarayya, Peter Lifu, domin ci gaba da shari’ar.
Tun da fari dai Nafiu Bala Gombe ya neman kotu ta hana Sanata David Mark, Rauf Aregbesola da sauran mambobin kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar gudanar da harkokin shugabancin ta, yana mai cewa nadin nasu ya saba wa kundin tsarin mulkin jami’iyyar ta ADC da kuma Dokar Zabe.
Sauyin alkalin ya biyo bayan umarnin da kotun ƙoli ta bayar na a gaggauta sauraron karar a Kotun Tarayya.
A baya, lauyoyin wadanda ake kara sun soki bukatar sauya alkalin, suna zargin mai karar da kokarin neman kotun da za ta fi masa anfani.
A baya dai tsohon shari’ar Emeka Nwite, ya dage sauraron karar har sai an samu cikakken kwafin hukuncin Kotun Koli.
