Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya gargaɗi dukkan ’yan siyasa da su guji liƙa fastocin yaƙin neman zaɓe a gadar sama, fitilun titi da sauran gine-ginen gwamnati, yana mai cewa duk wanda ya karya doka zai fuskanci hukuncin da ya dace.
Gargaɗin ya biyo bayan hukuncin da Kotun Majistare ta Jihar Adamawa ta yanke wa ɗan takarar gwamna na jam’iyyar ADC, Suleiman Umar, inda ta ci shi tarar Naira miliyan uku saboda liƙa fastocin yaƙin neman zaɓensa a gine-ginen gwamnati.
Mai magana da yawun gwamnan, Humwashi Wonosikou, ya bayyana cewa dokar kare kadarorin gwamnati ta shafi kowa da kowa, ba tare da la’akari da jam’iyya ko matsayi ba.
Ya ce gwamnati ba za ta amince da amfani da gadar sama, tsibirai, fitilun titi da sauran kadarorin jama’a wajen yaƙin neman zaɓe ba, domin an gina su ne da kuɗin al’umma kuma wajibi ne a kiyaye su.
Wonosikou ya ƙara da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da aiwatar da dokar ba tare da nuna bambanci ba, yana mai jaddada cewa shiga siyasa hakki ne na kowane ɗan ƙasa, amma lalata kadarorin gwamnati ba hakki ba ne.
Haka kuma, ya shawarci ’yan siyasa da su riƙa amfani da wuraren talla da aka amince da su, kafafen yaɗa labarai da sauran hanyoyin da doka ta tanada wajen gudanar da yaƙin neman zaɓensu.
