Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana cewa ba sai kundin tsarin mulkin ƙasa ya ba shi izini ba kafin ya ba Shugaban Ƙasa ko Gwamnan jiha shawara kan al’amuran da suka shafi ƙasa.
Sarkin ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin wani shiri na tashar Channel Television, inda ya ce a matsayinsa na jagoran al’umma, yana da hurumin bayar da shawarwari ga masu mulki kan abin da yake ganin ya dace domin ci gaban ƙasa.
Ya ce, “Shin sai an gaya mini ne kafin in ba Shugaban Ƙasa shawara? Shin sai kundin tsarin mulki ya gaya mini cewa idan na ga abin da bai dace ba, ba zan je wajen Shugaban Ƙasa in ce masa ‘Ranka ya daɗe, wannan abu ba daidai ba ne’?”
Sarkin ya ƙara da cewa ba ya buƙatar kundin tsarin mulki ya ba shi umarni kafin ya faɗa wa gwamna abin da ya dace a yi, yana mai cewa wannan hurumi yana samunsa ne daga kasancewarsa jagoran mutanen da yake shugabanta.
Ya jaddada cewa duk da cewa gwamnonin na da ikon zartarwa, hakan bai hana shugabannin gargajiya su ba da shawarwari domin gyaran al’umma ba.
Sarkin Kano ya kuma nanata muhimmancin shigar mata cikin harkokin siyasa da shugabanci, inda ya yi kira da a ƙara ba mata dama a muƙaman zaɓaɓɓu domin gina ƙasa mai adalci da haɗin kai.
A cewarsa, mata na taka muhimmiyar rawa wajen samar da shugabanci mai faɗi da haɗa kowa da kowa, kuma wajibi ne a ƙarfafa wakilcinsu a dukkan matakan mulki.
Har ila yau, Sarkin ya yi Allah-wadai da cin zarafi da tashin hankalin da ake yi wa mata a cikin al’umma, yana mai cewa babu wata al’ada da za ta halasta wa namiji dukan mace.
Ya ce tashin hankali ba na Afirka kaɗai ba ne, illa yana faruwa ne sakamakon rashin kariya ga mata da kuma amfani da iko wajen zaluntarsu.
Sarkin ya bayyana cewa mata, yara, talakawa da masu nakasa su ne mafi yawan waɗanda ke fuskantar tashin hankali a cikin al’umma, yana mai cewa dukkan ‘yan ƙasa mutane ne masu haƙƙoƙi da bai kamata a take su ba da sunan al’ada.
“Dole ne mu amince cewa muna da ‘yan ƙasa masu haƙƙoƙi, kuma waɗannan haƙƙoƙi ba za a tauye su ba ta kowace hanya, balle da sunan al’ada,” in ji Sarkin Kano.
