Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana alhininsa kan rasuwar fitaccen malamin sadarwa a Jami’ar Bayero Dr Musa Adamu Labaran, wanda ya rasu bayan gajeruwar rashin lafiya.
Hakan na kunshe ne cikin sakon ta’aziyyar da kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, inda gwamnan ya bayyana rasuwar Dr Musa a matsayin babban rashi ga bangaren ilimi, harkokin yada labarai da al’umma baki daya.
Gwamna Yusuf ya ce marigayin gogaggen masani ne kuma jagora a fannin sadarwa, wanda ya bayar da gudunmawa mai yawa wajen bunkasa ilimin sadarwa, gudanar da bincike da kuma horas da dalibai da kwararru da dama, inda ya bar kyakkyawan tarihi na nagarta, gaskiya da hidima ga al’umma.
Gwamnan ya ce rasuwar Dr Musa ta haifar da gibi mai girma a fannin ilimi da sadarwa, la’akari da irin gudunmawar da yake bayarwa wajen yada ilimi.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Abba na addu’ar Allah ya gafartawa marigayin, tare da baiwa iyalansa, abokan aikinsa, daliban sa, masoyansa da jami’ar Bayero hakurin jure rashin sa.
