Gwamnatin Japan ta ƙara tsaurara sharuɗɗan da baƙin ƙasashen da ke zaune a ƙasar za su cika kafin samun izinin zama na dindindin, ciki har da ƙwarewa a harshen Japan da fahimtar dokoki da al’adun zamantakewar ƙasar.
Sabbin ƙa’idojin sun tanadi cewa yawancin masu neman izinin za su nuna ƙwarewar harshen Japan a matakin B1 ko sama da haka, wanda zai ba su damar tattaunawa da gudanar da muhimman harkokin yau da kullum.
Haka kuma, hukumomin ƙasar za su tantance fahimtar masu neman izinin kan dokoki da tsarin zamantakewar Japan, domin tabbatar da cewa za su iya rayuwa da mu’amala da jama’a yadda ya kamata.
Sai dai sabbin sharuɗɗan sun tanadi keɓance wasu rukuni biyar daga sharadin harshen, ciki har da ƙwararrun ma’aikata na musamman, wasu daga cikin iyalansu, da mutanen da suka yi aƙalla shekaru shida na karatun firamare ko sakandare a Japan.
Bugu da ƙari, akwai wasu rukuni bakwai da za a iya sassauta musu sharuɗɗan, ciki har da ma’aurata da ‘ya’yan ‘yan ƙasar Japan, da mutanen da ke buƙatar kariya ta ƙasa da ƙasa.
Duk da wannan sassauci, hukumomin sun bayyana cewa ba za a amince da buƙatar kowa kai tsaye ba, domin za a ci gaba da tantance halayensa, yadda yake bin dokoki da kuma biyan haraji.
Yawancin sabbin ƙa’idojin za su fara aiki daga ranar 1 ga Afrilu, 2027, yayin da wasu sharuɗɗan da suka shafi kuɗin shiga suka fara aiki tun shekarar 2026.
