Shugaban Ƙaramar Hukumar Shanono Abubakar Barau Shanono, ya jagoranci sallar nafila, saukar Alƙur’ani da addu’o’i na musamman, domin neman Allah Ya kawo ƙarshen matsalar tsaro tare da tabbatar da zaman lafiya a Kano da yankin na su.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙaramar hukumar, Comrade Ammar Shanono, ya aikowa Premier Radio.
An gudanar da addu’o’in ne a Mazabar Dutsen Bakoshi, bisa umarnin Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, domin roƙon Allah Ya kawo ƙarshen hare-hare da sauran matsalolin tsaro da ke addabar wasu al’ummomin jihar.
A yayin addu’ar, an roƙi Allah Ya kare rayuka da dukiyoyin al’umma, Ya kawo ƙarshen hare-hare da sauran matsalolin tsaro, tare da dawo da cikakken zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Kano.
Shugaban ƙaramar hukumar ya samu rakiyar mataimakinsa, Mubarak Nasir Tsaure, Sakataren Ƙaramar Hukumar, Hon. Muntari Musa Shakogi, Shugaban Jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar, Alhaji Lawan Anaruwa, da sauran jagororin siyasa da na al’umma.
