Hukumomi a ƙasar Iran sun sanar da cewa za’a a binne tsohon jagoran addinin kasar, Ali Khameneia ranar 8 ga watan Yulin 2026 mai zuwa, watanni uku bayan mutuwarsa a hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai masa.
A cewar sanarwar da ofishin wallafa ayyukansa ya fitar, za’a fara gudanar da jana’izarsa a ranar 4 ga Yuli a Tehran, kafin a binne shi a ranar 8 ga watan Yuli a harabar masallacin Imam Reza da ke Mashhad.
Sanarwar ta ce za’a gudanar da jana’izar wasu daga cikin ’yan uwansa da suka mutu tare da shi a hare-haren, a garuruwa daban-daban da suka haɗa da Tehran, Qom da Mashhad.
Haka zalika, jami’ai sun bayyana cewa ana sa ran taron zai tara miliyoyin jama’a, inda aka tsara shirye-shirye na musamman ciki har da gangamin jama’a na kwanaki uku.
