Tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau ya sanar da ficewarsa daga jamʼiyyar PDP.
Shekarau ya bayyana haka ne a wata takarda mai dauke da sanya hannun sa da aka aike zuwa ga shugaban jam’iyyar na mazabar giginyu.
Dama a safiyar yau Shekarau ya kira taro na musamman a gidansa wanda zai gudana a Lahadin nan.
A taron ana hasashen Shekarau zai bayyana matsayinsa a cikin jam’iyyar PDP, bayan doguwar tattaunawa da shawara akan halin da siyasar Fadar Mundubawa da jihar Kano da Najeriya ke ciki.
Shekarau ya ce a matsayinsa na dan siyasa da ya sha alwashin ba zai daina ba, har karshen rayuwarsa, zai bayyana matsayinsa dana jama’ arsa akan halin da PDP ke ciki da matakan da ya dauka bayan shawara da tuntuba da abokan tafiya.
