Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya sanar da sabbin matakan tsaro da gwamnatin jihar ke fatan za su taimaka wajen dakile matsalar ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane da ke addabar sassan jihar.
Matakan sun hada da haramta sayarwa da jigilar man fetur a cikin jarkoki a fadin jihar, tare da wasu takunkumi da suka shafi harkokin kasuwanci da ake zargin suna taimaka wa masu aikata laifi.
A cewar kakakin gwamnan, Ibrahim Kaula Mohammed, matakan na kunshe ne cikin wata doka da aka zartar bayan wani taron gaggawa kan tsaro da ya hada jami’an tsaro, sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki.
“An dauki wannan mataki ne bayan rahotannin leken asiri da suka nuna cewa ana amfani da jigilar mai a jarkoki wajen tallafa wa ayyukan ‘yan bindiga a cikin dazuka,” in ji sanarwar.
A karkashin sabuwar dokar, an haramta saye, sayarwa, jigila da adana man fetur a jarkoki a fadin Katsina nan take.
Haka kuma, gwamnati ta umarci rufe dukkan wuraren POS da wuraren cajin waya a kananan hukumomin Matazu da Musawa, inda ake zargin wasu daga cikinsu na taimaka wa hanyoyin sadarwa da mu’amalar kudi na masu aikata laifi.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa an hana amfani da babura a wadannan yankuna biyu, domin rage zirga zirgar ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane.
“Mun dauki wannan mataki ne domin rage karfin motsi na masu aikata laifi da ke amfani da babura wajen kai hare-hare da kuma gudu,” in ji wani jami’in gwamnati.
Gwamna Radda ya jaddada cewa kare rayuka da dukiyoyin al’umma ne babban nauyin gwamnatinsa, yana mai cewa za a ci gaba da aiki kafada da kafada da jami’an tsaro.
Ya kuma yi kira ga al’umma da su bi sabbin dokokin tare da bayar da bayanan da za su taimaka wajen yakar rashin tsaro, tare da gargadin cewa duk wanda ya karya dokar zai fuskanci hukunci mai tsanani.
“Ba za mu lamunci karya wadannan dokoki ba. Za a dauki mataki mai tsauri kan duk wanda ya sabawa wannan umarni,” in ji sanarwar.
