Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce daga hawan sa mulki zuwa yanzu ya gudanar da ayyukan ci gaba da more rayuwa a jihar Kano, wanda kuɗin su ya zarce Naira tirilyan 9 da rabi.
Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da yake ƙaddamar da sashe na uku na babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna, da kuma Zariya zuwa Kano.
Shugaban wanda gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya wakilta, ya ce gwamnatin sa ta kammala titin ne wanda ta gada daga gwamnatin da ta gabata domin sauƙaƙa zirga-zirga, inganta tsaron matafiya da bunƙasa harkokin kasuwanci a jihar Kano da yankin Arewa maso Yamma.
Gwamnan ya kuma lissafa wasu ayyukan gwamnatin tarayya da ake gudanarwa a Kano, waɗanda suka haɗa da hanyoyin Kano zuwa Kaduna, Kano zuwa Maiduguri, hanyar Kano zuwa Katsina da layin dogo na Kano zuwa Maradi.
A nasa ɓangaren, Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta kammala aikin kilomita 118 na babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna, Zariya da Kano, a kan kuɗi naira biliyan 252.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito ministan na cewa daga cikin aikin hanyar, kilomita 81 anyi amfani da fasahar shimfiɗa siminti da rodika domin inganta aikin, wanda hakan zai inganta sufuri da bunƙasa tattalin arziki.
