Ƙungiyar Direbobin Motocin Haya ta ƙasa reshen Kano dake tashar Kofar Wambai ta roƙi Gwamnatin Jihar Kano da ta kafa kwamitin kar-ta-kwana domin sa ido kan tashoshin mota da ke ɗaukar fasinjoji ba bisa ƙa’ida ba.
Shugaban ƙungiyar tashar motoci ta Kofar Wambai, Alhaji Salisu Sani Yau Gareka, ne ya yi wannan kira a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishin ƙungiyar dake cikin tashar.
Alhaji Salisu ya ce ɗaukar fasinjoji a bakin titi na kawo cikas ga ci gaban harkar sufuri a jihar Kano, lamarin da ya ce ya daɗe yana damun masu sana’ar.
Ya ƙara da cewa ƙungiyar tashar Kofar Wambai za ta ci gaba da mara wa Gwamnatin Jihar Kano baya a duk wani shiri da zai kawo cigaban harkokin sufuri.
Haka kuma, ya shawarci direbobin haya a jihar Kano da su riƙa bin ƙa’idar shiga tashoshin mota don kaucewa asarar kudaden shiga na gwamnati.
