Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumi25 ga watan Afrilu ce ranar zazzaɓin cizon sauro ta Duniya' Alkaluma...

25 ga watan Afrilu ce ranar zazzaɓin cizon sauro ta Duniya’ Alkaluma na nuna cewa mutane 438,000 ne ke mutuwa a duk shekara sakamakon zazzabin cizon sauro.

Date:

A ranar L 25 ga watan Afrilun kowace shekara ne aka yi bikin ranar yaki da cutar zazzabin cizon sauro ta duniya na wannan shekara.

Majalisar dinkin duniya ce ta kebe wannan rana a duk shekara domin ganin an kawar da cutar daga doron duniyarmu.

Alkaluma na nuna cewa mutane 438,000 ne ke mutuwa a duk shekara sanadiyyar wannan cutar, kana mutane miliyan 214 na kamuwa da cutar, kuma kashi 90 cikin 100 na wadanda ke kamuwa da cutar ta malaria a nahiyar Afirka suke.

Masana harkar lafiya sun kuma bayyana cewa, muddin ba a dauki matakan da suka dace ba mutane da dama na fuskantar barazanar kamuwa da cutar a duniya.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bayyawa cewa, tun a shekarar 2015 kasashen Turai suka yi nasarar cimma burin kawar da cutar zazzabin cizon sauro.

Amma duk da irin wannan nasara da kasashen Turai suka cimma har yanzu cutar zazzabin cizon sauro na mummunar barna a kasashe masu tasowa, musamman kasashen Afirka da ke kudu da hamadar Sahara.

Hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta ce akwai kyakkyawan fatan kawar da cutar zazzabin cizon sauro a duniya baki daya, karkashin shirin da aka tsara a takardar fasahohin ba da jinya da rigakafin ciwon tun daga bana zuwa shekarar 2030 mai zuwa.

Latest stories

Related stories