Gwamnatin Iran ta bayyana cewa ba za ta shiga wata sabuwar tattaunawa da Amurka ba, tana mai karyata rahotannin da ke cewa ta nemi komawa kan teburin sulhu bayan hare-haren hadin gwiwa da Amurka da Isra’ila suka kai mata a karshen mako.
Wannan matsaya ta Tehran ta biyo bayan kalaman Shugaban Amurka, Donald Trump, wanda a ranar Lahadi ya ce ya amince da gudanar da tattaunawa da sabon shugabancin Iran duk da cewa hare-haren Amurka da Isra’ila kan kasar na ci gaba.
A hirarsa da mujallar The Atlantic, Trump ya ce, “Suna son yin magana, kuma na amince mu yi magana, duk da sun makara sosai,” in ji shi.
Daga baya kuma ya shaida wa NBC cewa jami’an Iran “na magana” da Amurka, ba tare da ya bayar da karin bayani ba.
Sai dai a martaninsa kan wannan, shugaban Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran, Ali Larijani, ya bayyana a ranar Litinin cewa Iran “ba za ta tattauna da Amurka ba.”
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, ya musanta rahotannin da ke cewa jami’an Iran sun nemi bude sabuwar hanyar tattaunawa da Washington.
Kalaman nasa na zuwa ne bayan wani sabon yanayi na tashin hankali da ya biyo bayan hare-haren hadin gwiwa da aka kai kan wasu muhimman wurare a Iran, lamarin da ya kara dagula alakar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu.
A wata sanarwa da ta fitar, gwamnatin Iran ta ce ba ta da niyyar komawa kan teburin sulhu a halin yanzu, tana mai jaddada cewa za ta ci gaba da daukar matakan mayar da martani kan manufofin Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya domin fansar hare-haren da aka kai mata.
Haka kuma, gwamnatin ta nuna cewa wannan matsayi ya zo ne a daidai lokacin da kasar ke cikin kwanaki 40 na makoki domin jimamin rasuwar jagoranta, Ali Khamenei, lamarin da ta ce ya kara tsananta yanayin siyasa da tsaro a yankin.
Sabon rikicin kalamai tsakanin Washington da Tehran na kara nuna tsanantar sabanin da ke tsakaninsu, yayin da kasashen duniya ke kira da a rage tashin hankali tare da komawa kan tattaunawa ta lumana domin kauce wa yaduwar rikici a yankin Gabas ta Tsakiya.
