Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya bayyana ranar damukradiyya a matsayin wata dama ta tunawa da muhimmancin mulkin dimokuraɗiyya da jajircewar al’umma wajen tabbatar da adalci, ‘yanci da ci gaba.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar don taya al’ummar jihar murnar zagayowar ranar.
Gwamna Yusuf ya ce gwamnatin sa ta mayar da hankali wajen samar da ribar dimokuraɗiyya ga al’umma, musamman ta hanyar aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da suka shafi ilimi, lafiya, hanyoyi da inganta rayuwar jama’a.
Gwamnan ya ce, ayyana dokar ta-baci a fannin ilimi ta haifar da ginawa da gyaran makarantu, ɗaukar sabbin malamai, samar da kayan koyo da koyarwa, biyan kuɗaɗen jarabawa da kuma tallafawa ɗalibai domin ci gaba da karatu a gida da ƙasashen waje.
A fannin lafiya kuwa, gwamnan ya ce an samu gagarumar nasara ta hanyar gyarawa da inganta cibiyoyin lafiya, ɗaukar ma’aikatan lafiya da kuma faɗaɗa ayyukan kula da lafiyar al’umma.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Yusuf na cewa gwamnatin sa tayi ayyukan ginawa da gyaran hanyoyi, samar da ruwan sha, tallafawa harkokin noma, ƙarfafa matasa da mata da kuma shirye-shiryen tallafawa marasa ƙarfi a cikin al’umma.
