
Aminu Abdullahi Ibrahim
Gwamnatin Iran ta ce rundunarta ta soji ta shirya wani sabon shiri na kare kanta da kuma mayar da martani cikin gaggawa idan Amurka ta sake kai mata hari.
Rahoton Al Jazeera ya ce hukumomin Iran sun bayyana cewa shirin da suka kira Maximum Deterrence zai haɗa da faɗaɗa jerin wuraren da za su iya kai wa hari, ciki har da kadarorin Amurka da Isra’ila a yankuna daban-daban.
Wannan na zuwa ne yayin da rikicin da ke tsakanin Iran da Amurka ke ci gaba da ƙara tsananta, duk da ƙoƙarin diflomasiyya na dakatar da faɗan.
A wani rahoto kuma, Hukumar Kula da Ayyukan Jiragen Ruwa ta Birtaniya, UKMTO, ta ce wani jirgin dakon mai ya gamu da hare-hare daga wasu abubuwa biyu da ba a san ko su wanene ba, a kusa da mashigar ruwa ta Hormuz.
A nata ɓangaren, Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran ta yi iƙirarin cewa wasu jiragen ruwa guda uku sun kama da wuta bayan sun taka nakiyoyin ruwa a mashigar.
Shugaban Amurka Donald Trump ya kuma danganta rikicin da Iran da rashin nasarar jam’iyyar Republican a zaɓen tsakiyar wa’adin shugabancin ƙasar.
Duk da waɗannan ikirari, akwai buƙatar a bambanta bayanan hukumomin Iran da bayanan da hukumomin kula da zirga-zirgar jiragen ruwa suka tabbatar, yayin da ake ci gaba da sa ido kan halin da ake ciki a yankin.
