Gwamnatin Kano ta buƙaci dukkannin matan da suka amfana da tallafin kuɗi na naira dubu 50-50 da take bayarwa duk wata, su tabbatar sun yi amfani da su ta hanyar farawa ko bunƙasa ƙananan sana’o’in da za su taimaka musu wajen dogaro da kai da inganta rayuwar iyalansu.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da rabon tallafin kudin ga mata 5,200 wadanda suka fito daga mazabu 484 na ƙananan hukumomi 44 dake Kano.
Gwamna Yusuf ya ce shirin bawa mata tallafin duk wata na daga cikin matakan gwamnatin jihar na ƙarfafa tattalin arzikin mata da rage talauci ta hanyar samar musu da jarin fara sana’a, tare da jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da ƙirƙiro shirye-shiryen da za su tallafawa mata da matasa domin bunƙasa sana’o’i da samar da ayyukan yi.
Wasu daga cikin matan da suka amfana da tallafin sun bayyana jin daɗin su ga gwamnatin ta kano bisa basu kudin, inda suka ce tallafin zai taimaka musu wajen faɗaɗa sana’o’insu da kuma ƙara samun kuɗaɗen shiga domin kula da iyalansu.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa gwamnan ya kuma yi kira ga waɗanda suka amfana da tallafin su guji karkatar da kudin zuwa wasu abubuwan da basu da amfani, kuma su tabbatar sun yi amfani da tallafin wajen gudanar da sana’o’in da za su inganta rayuwarsu.
