Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci kamfanonin sadarwa na MTN da Airtel su dawo da tsarin bashi na kati da data ga masu amfani dasu a Nijeriya.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, umarnin kotun ya dakatar da matakan da suka shafi dokokin bayar da rancen kuɗi ta yanar gizo da suka haddasa dakatar da wasu ayyukan kamfanonin.
A cikin ƙarar mai lamba, masu korafin sun yi zargin cewa waɗanda ake ƙara na shirin dakatarwa ta kowace hanya
Sun kuma bayyana cewa wannan shiri na ɗaukar mataki ya samo asali ne daga wasu umarni da ake zargin sun fito daga ƙa’idojin bada rance ta hanyar yanayar gizo.
