Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiƘungiyar malaman jami'o'i ta kasa ASUU ta ce ba za ta goyi...

Ƙungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU ta ce ba za ta goyi bayan shirin gwamnatin tarayyar na bai wa jami`o`i da manyan makarantu `yancin cin gashin-kai ba.

Date:

Ƙungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU ta ce ba za ta goyi bayan shirin gwamnatin tarayyar na bai wa jami`o`i da manyan makarantu `yancin cin gashin-kai ba.
Ƙungiyar malaman jami’o’in ta ce irin cin gashin-kan da gwamnatin tarayyar ke tunani ba zai kasance alheri ba ga ‘yan Najeriya.
Da yake Karin hasken kan dalilan rashin gamsuwa da matakin na gwamnatin tarayya shugaban kungiyar ta ASUU reshen jihar Kano Dr Abdulkadir Muhammad Dambazau y ace su cin gashin kan da suke nufi daban haka wanda gwamnati take nufi ita ma daban.

Maimakon haka Dr Abdulkadir Dambazau y ace kamata yayi gwamnati ta bar jami’oin su gudanar da ayyukan su na gudanarwa.

A wannan makon ne Ministan Ilimin ƙasar Farfesa Tahir Mamman, ya ce gwamnatin tarayyar na shirin fito da wasu sabbin hanyoyi ta yadda jami’o’i da manyan makarantun gwamnati za su dinga cin gashin kansu.

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...