Saurari premier Radio
23.5 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraikungiyar kwadago ta kasa NLC ta yi barazanar fara yajin aikin Sai...

kungiyar kwadago ta kasa NLC ta yi barazanar fara yajin aikin Sai Baba-ta-gani idan har gwamnatin tarayya ta gaza biyan bukatun ta a karshen wa’adin kwanaki 21 da zai kare nan da kusan mako guda

Date:

Bayan mako guda da jagorantar yajin aikin gargadi na kwanaki biyu a fadin kasar, a jiya Talata kungiyar kwadago ta kasa NLC ta yi barazanar fara yajin aikin sai baba-ta-gani idan har gwamnatin tarayya ta gaza biyan bukatun ta a karshen wa’adin kwanaki 21 da zai kare nan da kusan mako guda. .
Kungiyar kwadagon ta ce yajin aikin ya zama dole ne biyo bayan gazawar gwamnatin tarayya wajen samar da hanyoyin rage wa ‘yan Najeriya halin kuncin rayuwa sakamakon cire tallafin man fetur.
NLC ta kara da cewa matakin yajin aikin zai fara ne daga mako mai zuwa wanda kuma hakan zai haifar da dakatar da harkokin kasuwanci a fadin kasar.
Mataimakin babban sakataren kungiyar ta NLC, Mista Christopher Onyeka,yayin zantawar sa da manema labarai ya ce gwamnatin tarayya bai kamata a ce ta rabawa yan talakawa buhunan shinkafa ba yayin da kuma ta bawa kowanne dan majalisa tallafin miliyan 100.
A ranar 1 ga watan Satumba ne kungiyar ta bawa gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki 21 kan jinkirin rabon kayayyakin tallafin.
Sannan a ranar 5 da 6 ga watan Satumbar nan kungiyar ta gudanar da yajin aikin gargadi na kwanaki biyu.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...