Saurari premier Radio
35.9 C
Kano
Friday, June 14, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiƳan bunburutu na cin karen su ba babbaka sakamakon wahalar mai

Ƴan bunburutu na cin karen su ba babbaka sakamakon wahalar mai

Date:

Wahalar man fetur da ake fama da ita a kasar nan yanzu ta sa ‘yan bumburutu na sayar da lita guda tsakanin Naira dubu daya da metan zuwa dubu da dari uku.

Bincike ya nuna cewa ba ma a nan Kano kadai ba, gidajen mai da dama sun rufe a sassan ƙasar nan, yayin da waɗanda suke ɗan buɗewa kuma, ake shan baƙar wahala a layi kafin a samu.

Ana ci gaba da shan wannan wahala ne kuma duk da iƙirarin kamfanin mai na kasa ya yi cewa, ya shawo kan matsalar tun a shekaranjiya waccan.

Daga can birnin tarayya Abuja da wasu jihohi an tabbatar da cewa, gidajen man da ke sayar da fetur ɗin sun ƙara kuɗin lita zuwa N750, wasu kuma Naira 800.

Sai dai kuma, gidajen mai mallakin kamfanin mai na kasa NNPC na sayarwa a kan N617, amma akwai dogon layin da sai mai rabo ke iya samu.

Kawo yanzu dai ma’aikata da ’yan kasuwa a jihohin kasar nan na takawa a ƙasa, wasu kuma na biyan ninkin abun da a baya ake biya saboda wahalar da direbobi ke sha wajen samun man.

Latest stories

Related stories