Saurari premier Radio
36 C
Kano
Tuesday, June 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiƘungiyar manoma ta ƙaddamar da dalar masara a Kaduna

Ƙungiyar manoma ta ƙaddamar da dalar masara a Kaduna

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Ƙungiyar manoma ta kaddamar da dalar buhunan masara a jihar Kaduna, a wani yunƙuri da hukumomi ke cewa na nuna irin ci gaban da aka samu a ƙasar nan ta fuskar noman masarar.

Shirin dalar masara tsari ne na hadin-gwiwa tsakanin ƙungiyar manoman masara da Babban bankin kasa CBN, karkashin shirin bada tallafi ga manoma na Anchor Borrower Programme.

Ana sa ran tattara dalar da ta kai kimanin buhunan masara dubu dari biyar da aka karɓa daga manoma a faɗin ƙasar nan wadanda suka samu tallafin Anchor Borrower Programme.

Wannan na zuwa ne sama da mako biyu bayan shugaban kasa  Muhammadu Buhari ya yaye kallabin dalar buhunan shinkafa mafi girma da aka taɓa tattarawa a tarihin ƙasar nan in ji gwamnatinsa.

Shugaban kungiyar manoman masara ta kasa, Alhaji Bello Abubakar Funtuwa ya shaidawa maneman labarai cewa an tara dalar masarar ne don bayyana wa duniya irin nasarorin da aka samu a noman masara a a fadin kasar nan.

Ya ce rancen da ake bai wa manoma ya taka rawa wajen bai wa manoma damar tara irin wannan masara, kuma wannan somin-taɓi ne.

“Duk da cewa suna fuskantar matsalolin tsaro a kauyuka, hakan bai hanasu tara masara ba. Amma muna fatan tsaro ya inganta, saboda noman ya fi wanda aka gani a yanzu.”

Shirin na gwamnatin na zuwa ne adaidai lokacin da ‘yan kasa ke kokawa da yadda kayan abinci ke tashin gauron-zabi, inda a yanzu haka buhun masarar na kai wa dubu 22.

Latest stories

Related stories