Saurari premier Radio
24.2 C
Kano
Monday, September 9, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKane Ya Yaba Da Salon Kamun Ludayin Antonio Conte A Tottenham

Kane Ya Yaba Da Salon Kamun Ludayin Antonio Conte A Tottenham

Date:

Dan wasan gaba na Tottenham Harry Kane ya bayyana gamsuwa da salon kamun ludayin sabon manajan kungiyar Antonio Conte da ya maye gurbin Nuno Espirito Santo, bayan kai kungiyar ga nasara a wasan farko da ya jagorance ta.

A daren jiya Alhamis ne dai Tottenham ta yi nasarar lallasa Vitesse Arnhem da kwallaye 3 da 2 karkashin gasar Europa wanda ya bai wa magoya bayanta kwarin gwiwar yiwuwar Conte ya samar da sauyi a kungiyar mai fama da mashasshara.

Duk da cewa kwallo guda tal Kane ya iya zurawa a wasanni 9 da ya doka cikin wannan kaka, Kaftin din na Ingila ya ce da yiwuwar Tottenham ta murmure daga koma bayan da ta ke fuskanta karkashin jagorancin Conte wanda ya horar da kungiyoyin kwallon kafa na Juventus da Chelsea da kuma Inter Milan.

Shi kansa Antonio Conte yayin zantawarsa da manema labarai, ya ce ya na da kwarin gwiwar samar da gagarumin sauyi a kungiyar mai doka firimiya nan da dan wani lokaci.

Tottenham dai ta raba gari da Nuno wanda tsohon manajan Wolves ne watanni 4 bayan bashi ragamar kungiyar wadda rabonta da abin kirki tun bayan tafiyar Mauricio Pochettino wanda ya iya kaita har wasan karshe na cin kofin zakarun Turai a 2019.

Latest stories

Ni zan yi nasarar lashe zaben shugaban kasa a 2027 – Kwankwaso

"Ni zan yi nasarar lashe zaben shugaban kasa a...

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Ni zan yi nasarar lashe zaben shugaban kasa a 2027 – Kwankwaso

"Ni zan yi nasarar lashe zaben shugaban kasa a...

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...