Saurari premier Radio
31 C
Kano
Monday, April 29, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDambe na samun karbuwa

Dambe na samun karbuwa

Date:

Shirin Labarin Wasannin na wannan mako ya duba batun damben gargajiya da gasar Afcon da kuma gasar ATP ta wasannin kwallon tennis da Sabiya ta lashe.

Damben gargajiya a Najeriya:

A Tarrayyar Najeriya, damben gargajiya na kara samun karbuwa musamman arewacin kasar, inda matasa da dama suka dauki damben a matsayin sana’a, baya ga raya al’adar da aka gada daga kaka da kakkanni. ‘Yan dambe kamar Su Garkuwan Chindo da Bahagon Shagon ‘Yan Sanda da suka kama hanyar maye gurbin ‘yan damben da suka yi suna a da irin su Shagon Mafara da dan dunawa. A yanzu ma dai a Jihohi da dama ne ake gudanar da wasan Damben a Nigeria, ciki har da katsina inda wakilinmu Yusuf Ibrahim ya je daya daga gidajen Dambe don gane wa idanunsu kuma ya jiye wa kunnuwansa yadda ake wasa ‘yan damben. Kuna iya sauraren cikakken rahoton daga kasa a karshen rubutaccen labarin wasannin.

Shirye-shiryen gasar Afcon:

Shugaban Hukumar Kwallon kafa ta Afirka Ahmad Ahmad da tawagarsa sun isa Kamaru domin tattaunawa da hukumomin kasar dangane da lokacin da ya fi dacewa a gudanar da gasar wannan nahiya cikin shekara mai kamawa. Bisa ga jadawalin da aka tsaida dai, a watan Yuni da Yuli ne ya kamata a shirya gasar AFCON ta 2021, amma akwai yiwuwar sake maida ta cikin watanni Janairu da Fabrairu kamar yadda aka saba a baya sakamakon ruwan sama da aka saba shatatawa a Kamaru a lokacin bazara. Wani dalilan da zai haddasa wannan canji shi ne gasar Kwallon Kafa ta kulob-kulob din kasashen duniya wacce aka shirya gudanarwa a watan Yuni da Yuli 2021.

Tawagar ta CAF za ta yi amfani da wannan dama wajen gane wa idanunta inda aka kwana wajen shirya gasar kwallaon kafa ta Afirka ta ‘yan wasa da ke bugawa a gida da za ta gudana a kasar Kamaru a cikin ‘yan makonni masu zuwa. Kazalika manyan jami’an na Hukumar Kwallon Kafar Afirka za su san ko Kamaru ta shirya wajen daukar bakuncin kasan, wanda ya kamata ta shirya a 2019 amma jinkiri ya sa aka danka wa Masar. A ranar Laraba ne jami’a na kwallon kafar Afirka da hukumomin Kamaru za su sanar da shawarwarin hadin gwiwa da suka yanke dangane da lokacin gudanar da AFCON na 2012.

Latest stories

Related stories