Saurari premier Radio
32.9 C
Kano
Friday, June 14, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiƘungiyar Hamas ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.

Ƙungiyar Hamas ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.

Date:

Jagorancin kungiyar Hamas ya ce sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta shaida wa masu shiga tsakani na kasashen Qatar da Egypt dangane da shawarar amincewar.

Kawo yanzu dai babu cikakken bayani dangane da yarjejeniyar da suka hada da tsawon lokacin tsagaita wuta da kuma makomar mutanen da Hamas suka yi garkuwa da su a Gaza.

Jami’an kungiyar ta Hamas na cewa yanzu zaɓi ya ragewa Isra’ila tunda su sun amince da sharuɗɗan yarjejeniyar.

A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, shugaban Hamas, Isma’il Haniyeh ya kira firaministan Qatar, Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al-Thani da kuma ministan bayanan sirri na Egypt, Abbas Kamel inda ya sanar da su dangane da amincewar da Hamas ɗin ta yi da yarjejeniyar tsagaita wutar.

To sai dai Isra’ila a nata bangaren, ta ce tana ci gaba da bin diddigin abubuwan da ke faruwa a kowane bangare game da ƙudirin tsagaita wuta a Zirin Gaza da Hamas ta amince da shi.

Mai magana da yawun rundunar sojin Isra’ila, Daniel Hagari, ya faɗa wa taron manema labarai cewa suna duba daftarin abin da Hamas ta saka wa hannu.

Latest stories

Related stories