Wasu ’yan bindiga sun kai hari garin Dukura da ke ƙaramar hukumar Kebbe a jihar Sokoto, inda suka kashe mutane biyu tare da kwashe dabbobi da babura mallakar mazauna yankin, lamarin ya faru ne ranar Litinin.
Rahotanni sun ce ’yan bindigar sun tare hanyar da ta haɗa wasu garuruwa da kasuwar Tambuwal, kafin su fara kwashe shanu, raƙuma, tumaki da kuma wasu babura na masu sana’ar adaidaita sahu.
Lamarin ya ƙara haifar da fargaba a Dukura da Dalijan, da kuma wasu ƙauyuka da ke unguwar Girkau, ciki har da Zugu, Indire, Mazoji, Tungar Kabawa da Runtuwa.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Sokoto, DSP Ahmed Rufai, ya tabbatar da harin, inda ya ce jami’an tsaro sun samu labarin abin da ke faruwa kuma tuni suka kai ɗauki yankin.
Ya ce bayan isarsu, jami’an ’yan sanda sun yi musayar wuta da maharan, lamarin da ya tilasta musu ja da baya, sai dai kafin isowar jami’an tsaron, ’yan bindigar sun riga sun kashe mutane biyu tare da kwashe wasu dabbobi.
Rundunar ta ce tana ci gaba da tattara bayanai tare da ƙarfafa tsaro a yankunan da abin ya shafa.
