Kungiyar kare hakkin bil’adama ta international human right commission tare da hadin gwiwar wasu kungiyoyi sun gudanar da bincike inda suka gano karancin albashi da rashin walwalar jamia’an tsaro na daya daga cikin dalilan da ke haddasa cin hanci ga jami’an da tabarbarewar tsaro a Najeriya.
Shugaban kungiyar Ambasada Abdullahi Bakoji Adamu ya kuma bukaci gwamnati da hukumomin bincike da su gudanar da cikakken bincike kan abubuwan da ke iya haifar da cin hanci da rashawa a wasu hukumomin tsaro.
Bakoji ya ce rashin wadataccen albashi da walwalar jami’an tsaro, da kuma karancin kayan aiki, na iya jefa wasu jami’ai cikin matsin lamba wajen gudanar da ayyukansu.
Kungiyar ta kuma bukaci gwamnati ta yi bincike kan zargin cewa akwai wasu hukumomin tsaro da suke matsawa wasu shugabannin matakai ko na jihohi wajen samar da kudade.
Kungiyar ta kuma ce bata bayyana zargin a matsayin tabbataccen laifi ba sai dai ta bukaci gwamnati da ta yi kyakkawan bincike kan zargin domin gano gaskiya da kuma hukunta masu laifukan.
