Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya ce tattalin arzikin Najeriya da ya riga ya durƙushe idan ba don matakan da Bola Tinubu ya ɗauka ba .
Shettima ya bayyana hakan ne a zauren liyafa na fadar shugaban ƙasa, yayin wani taro da ƙungiyar City Boy Movement ta shirya.
Shettima ya amince cewa ’yan Najeriya sun sha wahala, amma ya yi hasashen farashin kayan abinci zai ragu nan da makonni masu zuwa saboda sabbin matakan noma .
Ya ce ajiyar kuɗaɗen waje ta Najeriya ta kusa dala biliyan 60, yayin da tattalin arzikin ƙasar ya bunƙasa da kashi 4.43 cikin ɗari.
Ya kuma roƙi matasa da su fita su isar da saƙon sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa ga sauran ’yan Najeriya.
