Farashin ɗanyen mai ya sake tashi, sakamakon rufe wani muhimmin bututun mai a Saudiyya da kuma hare-haren jiragen ruwa a yankin Gulf.
Farashin ɗanyen mai na Brent ya haura zuwa dala 108 kan kowace ganga jim kaɗan bayan da kasuwa ta buɗe.
Saudiyya ta ce ta rufe bututun man da ke haɗa gabas maso yammacin ƙasar, bayan wasu jirage marasa matuƙa da aka harba daga yankin Iraq sun kai hari tare da lalata bututun.
A baya, Saudiyya ta zargi ƙungiyoyin mayaƙan da Iran ke marawa baya da hannu wajen kai irin waɗannan hare-hare.
A wani ɓangare kuma, Oman ta ɗage wani taron da aka shirya gudanarwa ranar Litinin tsakanin Iran da ƙasashen Larabawa na yankin Gulf domin tattauna batutuwan da suka shafi Mashigar Hormuz.
