Gwamnan Jihar Oyo kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APM, Seyi Makinde, ya yi alkawarin yin wa’adi ɗaya na shekaru huɗu kacal idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasar Najeriya a 2027.
Makinde ya bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa tsakanin jam’iyyar APM da al’umma a yankin Arewa maso Gabas, wanda aka gudanar a Jihar Adamawa.
Ya ce gwamnatinsa za ta kasance ta haɗin kan ’yan Najeriya, wadda za ta haɗa kowane ɓangare na ƙasar nan, tare da mayar da hankali kan gaskiya da riƙon amana wajen tafiyar da mulki.
Gwamnan ya kuma ƙalubalanci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya bayyana tsarin da gwamnatin tarayya ke amfani da shi wajen ƙayyade farashin man fetur.
Makinde ya soki wasu manufofin gwamnatin Tinubu, ciki har da amfani da iskar gas ta CNG, motocin lantarki da kuma shirin musayar ɗanyen mai da naira, yana mai cewa waɗannan matakai ba su samar da sakamakon da ake tsammani ba.
Ya kuma tunatar da shugaban ƙasar alƙawarin da ya ɗauka na inganta samar da wutar lantarki cikin shekaru huɗu, yana mai cewa zaɓen 2027 ya kamata ya kawo ƙarshen siyasar yaudara da rashin cika alƙawura.
A cewarsa, jam’iyyar APM za ta tsara manufofinta ne bayan sauraron ra’ayoyin masu ruwa da tsaki, domin tabbatar da cewa shirinta na tafiyar da ƙasa ya dace da buƙatun ’yan Najeriya.
