Shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na da tabbacin samun nasara a jihohi sama da 20 a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
Tsohon gwamnan Jihar Zamfara ya bayyana hakan ne bayan ganawarsa da Shugaba Tinubu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, inda suka tattauna kan jadawalin yaƙin neman zaɓen da kuma ziyarar da shugaban ƙasar zai kai wasu jihohi.
Sanata Yari ya kuma yi ikirarin cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, da na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ba su da tabbacin samun cikakken rinjaye a wata jiha a wajen yankunansu.
Ya ƙalubalanci Atiku Abubakar da ya bayyana jihar da jam’iyyar ADC ke da ƙarfin lashe zaɓe a Kudancin Najeriya.
A cewarsa, ko da ɗan takara ya samu goyon bayan kashi 80 cikin 100 na masu zaɓe a Kudancin ƙasar, hakan ba zai wadatar wajen samun nasara ba idan bai samu goyon baya a Arewa ba.
Haka kuma, ya ce samun irin wannan gagarumin goyon baya a Arewa ba zai wadatar ba idan ɗan takara bai samu goyon baya a Kudancin ƙasar ba.
