Gwamnatin Tarayyar ta bayyana sunayen wasu mutane da take zargi da shirya kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu a wani yunkurin juyin mulki da bai yi nasara ba..
Takardun karar da aka shigar a gaban babbar kotun tarayya dake Abuja ta nuna cewa daga cikin wadanda ake zargi akwai tsohon gwamnan jihar Bayelsa State, Timipre Sylva, wanda aka ce yana gudun hijira.
Sauran sun hada da Manjo Janar Mohammed Ibrahim Gana, Kyaftin Erasmus Ochegobia Victor, Sufeto Ahmed Ibrahim, Zekeri Umoru, Bukar Kashim Goni da Abdulkadir Sani.
A cikin tuhume tuhume 13 Gwamnatin tarayya ta zargi mutanen da kitsa tayar da yakin basasa domin hambarar da shugaban kasa.
Laifin na karkashin sashe na 37(2) na dokar laifuffuka ta kasa.
Ana sa ran gurfanar da wadanda ake zargin a gobe Laraba 22 ga Afrilu, 2026, a gaban Mai shari’a Joyce Abdulmalik.
Ofishin Ministan Shari’a na tarayya ne ya shigar da karar, inda Daraktan gabatar da kara na kasa, Rotimi Oyedepo, SAN, ya sanya hannu.
Gwamnatin ta kuma tuhumi wadanda ake zargin da laifukan ta’addanci, boye bayanan sirri na tsaro, da kuma safarar kudaden da ake alakantawa da tallafa wa ayyukan ta’addanci.
A cewar masu gabatar da kara, wadanda ake zargin sun san da wani shirin tayar da kayar baya da wani Kanar Mohammed Alhassan Ma’aji da wasu ke shiryawa, amma suka kasa sanar da hukumomi.
Baya ga zargin juyin mulki, ana kuma tuhumar su karkashin dokar yaki da ta’addanci ta shekarar 2022.
