Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai, zai sake gurfana a gaban babbar kotun tarayya da ke Kaduna a yau domin sauraron bukatar bayar da belin sa.
An tsare El-Rufai na sama da wata guda kafin hukumar (ICPC) ta gurfanar da shi a gaban Mai Shari’a Rilwan M. Aikawa bisa tuhume-tuhume guda goma.
Zarge-zargen sun hada da mallakar kadarorin gwamnati ba bisa ka’ida ba, karkatar da su, da kuma halasta kudaden haram (money laundering).
Tun da farko kotun ta tsayar da ranar 31 ga Maris 2026 domin sauraron bukatun da ke gaban ta, ciki har da bukatar neman belin da tsohon gwamnan ya gabatar.
Sai dai a ranar 27 ga Maris 2026, ICPC ta amince da sakin El-Rufai na wucin gadi bisa dalilai na jin kai, bayan rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Umma El-Rufai, a birnin Cairo na kasar Masar.
Ana sa ran zaman kotun zai cigaba a yau bayan kammala jana’izar marigayiyar.
