Ƙungiyar likitoci masu neman kwarewa ta kasa ta yi barazanar shiga yajin aiki idan gwamnati ba ta ɗauki matakan da suka dace ba wajen dakile cin zarafi da ake kai wa ma’aikatan lafiya a faɗin ƙasar nan.
Ƙungiyar ta bayyana cewa, aƙalla manyan cibiyoyin lafiya 17 sun fuskanci hare-hare kan likitoci, ma’aikatan jinya da sauran ma’aikatan lafiya cikin shekara guda da ta gabata.
Ta ce sama da kashi 90 cikin 100 na waɗanda abin ya shafa mambobinta ne, inda suka gamu da raunuka da asarar dukiya.
Ƙungiyar ta ce idan har zuwa ƙarshen taronta na shekara ba a ɗauki matakai masu gamsarwa ba, wajen hukunta masu aikata irin waɗannan cin zarafi ba, ba za ta iya tabbatar da zaman lafiya a fannin kiwon lafiya ba bayan taron.
Ƙungiyar ta koka da cewa galibin waɗanda aka kai wa hari suna samun wasiƙar neman afuwa kawai daga masu laifi, ba tare da an hukunta su yadda ya kamata ba.
Ƙungiyar ta jaddada cewa rayukan likitoci da sauran ma’aikatan lafiya suna da muhimmanci, tana mai kira ga gwamnati da hukumomin tsaro su ɗauki matakan gaggawa domin kawo ƙarshen wannan matsala.
