Gwamnatin Kano ta bada umarnin dakatar da sare bishiyoyi ba tare da izini ba a harabar gidan talabijin na Abubakar Rimi ARTV, bayan bullar wani faifan bidiyo da ya nuna yadda ake sare bishiyoyi a harabar gidan talabijin din.
Kwamishinan yada labarai Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayar da umarni yayin wata ziyarar bazata da ya kai tashar.
Wayya ya ce sare bishiyoyi ba biss ƙa’ida ba ya saɓawa manufofin gwamnatin Kano na kare muhalli da yaƙi da sauyin yanayi, tare da yin gargaɗi cewa kar sake yunƙurin sare wata bishiya a harabar ta ARTV sai an samu izini daga hukumomin da abin ya shafa.
Kwamared Waiya ya bayyana damuwa kan yadda ARTV din ta gaza biyan bukatun masu kallo sakamakon tsofaffin shirye-shirye da ƙarancin ingancin shirya labarai, inda ya ce zamani ya zo da ci gaba a fannin sadarwa, din haka ARTV na buƙatar sabunta ayyukanta don yin gogayya da sauran takwarorin ta a Najeriya, musamman wajen samar da damar kallon shirye-shirye ta hanyoyin zamani da mu’amala kai tsaye da masu kallo.
Kwamishinan ya yi alƙawarin gabatar da rahoto na musamman ga gwamnan Kano domin samarwa ARTV tallafi na musamman da zai taimaka wajen inganta kayan aiki da tsarin gudanarwar ta, tara da buƙatar mahukuntan tashar su mayar da hankali wajen amfani da kasafin
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Mataimakin Shugabar tashar ARTV din, Malam Idris Abba Musa, ya bayyana cewa tashar na fuskantar ƙalubalen da suka haɗa da matsalolin gudanarwa, ƙarancin horas da ma’aikata da kuma buƙatar ƙarin inganta kayan aikin zamani na tashar.
