Hukumar Shari’a ta Kano da hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa, NDLEA, reshen jihar, sun tattauna hanyoyin ƙarfafa haɗin gwiwa domin yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi da fataucinsu a faɗin jihar.
Hakan na ƙunshe ne a ziyarar da tawagar Hukumar Shari’a ta kai hedikwatar NDLEA ta Kano, inda ta gana da kwamandan hukumar na jihar, Ɗahiru Yahaya Lawal.
Da yake jawabi yayin ziyarar, Kwamishina na biyu a Hukumar Shari’ar ta Kano, Sheikh Ali Ɗan abba, ya ce manufar ziyarar ita ce ƙulla alaƙar aiki da NDLEA, domin haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen rage shan miyagun ƙwayoyi da dakile fataucinsu.
Sheikh Ali Ɗanabba ya kuma yaba da ƙoƙarin kwamandan NDLEA na Kano, Ɗahiru Yahaya Lawal, wajen yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi da sauran kayan maye.
A nasa ɓangaren, kwamandan NDLEA na Kano, Ɗahiru Yahaya Lawal, ya nuna godiya kan ziyarar, tare da buƙatar limaman masallatai da su ƙara himma wajen wayar da kan al’umma game da illolin miyagun ƙwayoyi, musamman ta hanyar huɗubobin Juma’a.
