Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, yayi ta’aziyyar rasuwar shahararren dan kasuwa, Alhaji Abdullahi Ahmad, wanda aka fi sani da Audu Manager, a wani asibiti da ke birnin Alkahira na kasar Masar bayan fama da rashin lafiya.
Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar.
Gwamna Abba ya bayyana marigayin a matsayin fitaccen dan kasuwa wanda gudunmawar da ya bayar wajen bunkasa harkokin kasuwanci, ci gaban tattalin arziki da ayyukan taimakon al’umma za su ci gaba da kasancewa abin tunawa a Kano da Arewacin Najeriya baki daya.
Gwamnan ya ce marigayin yayi fice wajen jajircewa, rikon amana da sadaukar da kai wajen habaka harkokin kasuwanci, lamarin da ya samar da ayyukan yi da hanyoyin samun abin dogaro ga jama’a da dama.
Gwamna Abba ya bayyana rasuwar Audu Manager a matsayin babban rashi ga iyalansa, al’ummar ‘yan kasuwa da kuma Kano baki daya, duba da irin rawar da ya taka wajen bunkasa tattalin arziki da ayyukan jin kai.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Yusuf yana mika ta’aziyyarsa a madadin gwamnati da al’ummar Kano ga iyalan marigayin, abokansa, abokan hulda da daukacin al’ummar ‘yan kasuwa.
