
Aminu Abdullahi Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da aikin kidayar makarantu ta shekarar karatu ta 2025/2026 (Annual School Census – ASC), inda ta sake jaddada aniyarta ta amfani da sahihan bayanai wajen tsara ingantattun manufofi da shirye-shiryen bunƙasa fannin ilimi.
Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da shirin tare da raba takardun tattara bayanai ga hukumomi da sassa ƙarƙashin Ma’aikatar Ilimi a ranar Alhamis, Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dakta Gwani Ali Abubakar Haruna Makoda, ya ce ingantattu kuma amintattun bayanai su ne ginshiƙin tsara manufofin ilimi da aiwatar da su yadda ya kamata.
Ya bayyana cewa kidayar makarantu ta shekara za ta bai wa gwamnati damar samun bayanan da ake buƙata domin samar da manufofi masu kyau kan ginawa da gyaran makarantu, rabon malamai, yawan ɗalibai masu shiga makaranta, kasafin kuɗi da sauran muhimman fannoni na ilimi.
Kwamishinan ya umarci dukkan ma’aikatu, sassa da hukumomin da ke ƙarƙashin ma’aikatar Ilimi da su tabbatar sun kammala cike takardun tattara bayanan tare da miƙa su kafin makon farko na watan Agustan 2026, domin a tattara tare da ɗora bayanan a tsarin bayanan ilimi na ƙasa cikin lokaci.
Samarwa Matasa Ilimin Fasaha, Zai Haɓaka Tattalin Arzikin Nijeriya – Masfo Global
Makoda ya tuna cewa Jihar Kano ce ta zo ta farko a ƙasar nan a aikin Ƙidayar Makarantu da ya gabata, inda ya buƙaci jami’an da ke gudanar da aikin na wannan shekarar su ci gaba da riƙe wannan matsayi.
Ya kuma yaba wa abokan hulɗar ci gaba bisa ci gaba da bayar da tallafin fasaha da na kuɗi domin ƙarfafa tsarin gudanar da bayanan ilimi a jihar.
Kwankwasiyya ta soki matakin rushe ma’aikatar ilimi mai zurfi a Kano
Haka kuma ya yabawa hukumar kula da makarantu masu zaman kansu da na sa-kai ta Jihar Kano da sauran hukumomin ma’aikatar saboda ƙwazon da suka nuna a aikin ƙidayar da ya gabata, tare da ƙarfafa musu gwiwa su maimaita wannan nasara.
A nasa jawabin, babban sakataren Ma’aikatar Ilimi, Alhaji Bashir Baffa, ya buƙaci dukkan hukumomin da ke ƙarƙashin ma’aikatar su ƙara ƙaimi wajen tattarawa da miƙa sahihan bayanai, yana mai cewa ingancin tsare-tsaren gwamnati ya dogara ne da sahihancin bayanan da ake samu.
Shi ma Daraktan Tsare-tsare, bincike da kididdiga na ma’aikatar, Alhaji Yushau Hamza Kafinchiri, ya bayyana cewa za a tattara bayanan ne ta hanyar takardun tambayoyi da aka tanada kafin a ɗora su a dandalin bayanan ilimi na ƙasa.
Ya ce ana sa ran kammala tattara dukkan bayanan kafin makon farko na watan Agusta, tare da gode wa shugabannin hukumomi bisa haɗin kan da suka bayar a aikin da ya gabata, yana mai roƙonsu su ci gaba da bayar da irin wannan goyon baya.
Sakataren zartarwa na hukumar Kula da makarantu masu zaman kansu da na sa-kai ta Jihar Kano, Alhaji Baba Umar, ya bayyana cewa hukumar ta fara tattara bayanan tun tuni, kuma ya nuna ƙwarin gwiwar cewa za a kammala aikin cikin mako guda.
A nasa bangaren, wakilin UNICEF, Umar Muhammad, ya bayyana fatan cewa za a kammala tattara bayanan kafin ƙarshen zangon karatun da ake ciki.
Ya ce za a shirya horaswa ta kwanaki biyu ga masu tattara bayanai kan yadda za su ɗora su daidai a dandalin bayanan ilimi na ƙasa, tare da roƙon Hukumar Kula da Makarantu Masu Zaman Kansu da na Sa-kai ta raba takardun tambayoyin kafin ƙarshen zango na uku.
Haka kuma, wakilin Plan International, David, ya ce sakamakon Ƙidayar Makarantu ta Shekara na ƙara inganci da sahihanci ga tsare-tsaren ilimi da tsara manufofi. Ya tabbatar da cewa ƙungiyarsu za ta ci gaba da bai wa gwamnatin jihar goyon baya domin tabbatar da nasarar gudanar da aikin.
