
Aminu Abdullahi Ibrahim
Tsohon gwamnan jihar Borno kuma jigo a jam’iyyar APC, Ali Modu Sheriff, ya ce ya kamata tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya dakatar da burinsa na tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027, yana mai cewa har yanzu wa’adin mulki na Kudu ne.
Sheriff ya bayyana hakan ne a shirin Politics Today na tashar Channels Television, inda ya ce akwai wata yarjejeniya ta raba madafun iko tsakanin yankunan ƙasar da aka cimma bayan yaƙin basasa domin tabbatar da daidaito.
A cewarsa, bayan shugaba Muhammadu Buhari, ya kammala wa’adin shekaru takwas daga Arewa, ya dace Kudu ta ci gaba da riƙe shugabancin ƙasa.
“Atiku jagora ne a Arewa kuma ya cancanci zama shugaban ƙasa, amma yanzu ba lokacin Arewa ba ne. Ya kamata ya jira zuwa 2031,” in ji Sheriff.
Ya kuma bayyana kwarin gwiwar cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai sake lashe zaɓen 2027, duk da cewa APC ba za ta yi sakaci ba wajen tunkarar zaɓen.
Game da tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, Sheriff ya ce bai damu da takararsa ba, yana mai ikirarin cewa ‘yan Arewa ba za su goyi bayansa ba.
Ya kuma yi zargin cewa lokacin da Obi yake gwamnan Anambra, ya kori ‘yan Arewa daga jihar.
Sheriff ya ƙara da cewa wasu magoya bayan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a Kano ba sa son a yi wata haɗaka da Peter Obi.
Kalaman Sheriff na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa da sauya sheƙar ‘yan siyasa gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
