
Aminu Abdullahi Ibrahim
Tsohon Gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya soki tsohon gwamnan jihar Borno, Ali Modu Sheriff, kan kalamansa cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party a zaɓen 2023, Peter Obi, ba zai samu goyon bayan ‘yan Arewa a zaɓen 2027 ba.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Kwankwaso ya ce ya kalli hirar Sheriff da tashar Channels TV cikin takaici, yana mai cewa kalaman tsohon gwamnan ba su dace da halin da siyasar Arewa ke ciki ba.
Ya ce bayan dogon lokaci da Sheriff ya ɗauka ba tare da yin magana a bainar jama’a ba, ana sa ran hakan zai ƙara masa hangen nesa, amma abin takaici hakan bai faru ba.
Kwankwaso ya kuma yi watsi da ikirarin Sheriff cewa Peter Obi ba zai samu goyon bayan Arewa ba, yana mai cewa Obi ya samu kusan ƙuri’u miliyan 2.8 a jihohin Arewa a zaɓen shugaban ƙasa na farko.
Ya ƙara da cewa matsin tattalin arziki da zamantakewar al’umma da ake ciki a yanzu, tare da abin da ya bayyana a matsayin gazawar gwamnatin mai mulki, sun ƙara wa haɗakar “OK Ticket” ƙarfin gwiwa a Arewa.
Har ila yau, ya musanta ikirarin Sheriff cewa al’ummar Kano ba za su goyi bayan Peter Obi ba, yana mai cewa a tarihi, al’ummar Kano na mara wa duk ɗan takarar da tafiyar Kwankwasiyya ta amince da shi baya, ba tare da la’akari da yankinsa ko ƙabilarsa ba.
Kwankwaso ya bukaci Ali Modu Sheriff da ya fi mayar da hankali kan matsalar rashin tsaro da ta addabi jihar Borno da Arewa maso Gabas, maimakon yin kalaman siyasa kan zaɓen 2027.
