Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiYara 100 sun zama marayu sakamakon kone masallata sama da 30 a...

Yara 100 sun zama marayu sakamakon kone masallata sama da 30 a Kano.

Date:

Bayanai na tabbatar da cewa, yara 100 ne suka zama marayu sakammakon bankawa iyayensu wuta a masallacin kauyen Larabar Abasawa dake karamar hukumar Gezawa a jihar Kano.

Idan ba’a manta ba wani mutum ya zubawa masallata man fetur a kwanakin baya, abinda yayi sanadin kone masallata sama da 30 da kuma mutuwar 15 daga cikinsu.

Hakan ya sa yara 100 sun zama marayu, matan aure 13 suka zama zawarawa sakammakon harin da matashi mai shekara 38 ya kai wannan masallaci.

An hakikance cewa, mutane 15 sun rasa rayukansu daga cikin wadanda harin masallacin ya rutsa da su, inda a halin yanzu ake zaman makoki a unguwar Gidan Goro da ke kauyen.

Sama da mutane 30 dake jam’in sallar aAsuba a masallacin, lokacin da Shafi’u, wanda ake zargi ya shiga ciki ya sanya man fetur tate da cinna wuta.

Majiyoyi a kauyen da hukumomin tsaro, sun ce rikicin gado ne da ya ki-ci-ya-ki-cinyewa a dangin matashin ya sa shi wannan danyen aiki.

Yanzun haka dai Shafi’u na hannun ’yansanda, wadanda ya mika kansa garesu bayan ya yi wannan aika-aika Larabar makon jiya.

Latest stories

Related stories