Saurari premier Radio
32.9 C
Kano
Friday, June 14, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumi'Yan Majalisar Dokokin Amurka 16 Sun Rubuta Wasiƙar Koke Zuwa ga Shugaban...

‘Yan Majalisar Dokokin Amurka 16 Sun Rubuta Wasiƙar Koke Zuwa ga Shugaban ƙasar, Joe Biden, Kan Gwamnatin Najeriya ta Sake Tigran Gambaryan, Don ya Koma Gida Amurka.

Date:

Yayin da jamian tsaron kasar nan ke cigaba da tsare shugaban kamfanin hada-hadar kuɗin Kirifto na Binance, Tigran Gambaryan, sakamakon wasu laifuka masu alaka da kudi, wasu ‘yan majalisar dokokin Amurka 16 sun rubuta wasiƙar koke zuwa ga shugaban ƙasar, Joe Biden, suna neman gwamnatin Najeriya ta sakeshi don ya koma gida Amurka

‘Yan majalisar sun yi zargin cewa Mista Gambaryan na cikin mawuyacin hali a inda ake tsare da shi  a kasar nan.

Gwamnatin Najeriya ce dai ta kama shugaban kamfanin na Binance, kuma ta tuhume shi tare da kamfanin nasa, game da rashin biyan harajin sayen kayayyaki na VAT da sauran wasu laifuka.

A cewar gwamnatin Najeriyar  ana bin matakan da suka kamata a shari’ar da ake yi masa bisa tsarin dokokin ƙasar nan.

‘Yan majalisar dokokin na Amurka 16 da sun ce suna magana ne da yawun iyalan shugaban kamfanin na Binance, Mista Tigran Gambaryan, da sauran Amurkawan da abin ya dama, inda suka buƙaci gwamnatin Najeriya ta gaggauta mayar da shi Amurka.

Saboda a ganin su ana tsare da shi ne ba bisa ƙa’ida ba, cikin wani mummunan yanayi, da kuma rashin ƙoshin lafiya, abin da suke ganin yana cike da hatsari ga rayuwarsa.

Idan za’a iya tunawa a cikin watan Fabrairun da ya gabata ne gwamnatin tarayyar kasar nan ta cafke shugaban kamfanin na Binance, tare da shugaban kamfanoin nasa a nahiyar Afirka, Nadeem An-jar-walla, wanda ya tsere a ranar 22 ga watan Maris da ya gabata, daga inda jami’an tsaro ke tsaro da su.

 

Latest stories

Related stories