
Aminu Abdullahi Ibrahim
Shugabar hukumar Dakta Binta Abubakar ce ta bayyana haka yayin taron bita da aka shiryawa daraktoci da ma’aikatan hukumar domin karfafa yadda suke gudanar da aiki.
Ta ce hukumar zata tabbatar da cewa an samu karuwar mutane masu ilimi musamman wadanda basu samu damar zuwa makaranta a lokacin da ya dace ba.
Dakta Binta hore su da su yi amfani da ilimi, ƙwarewa da gogewar da suka samu wajen inganta aikinsu.
Da yake magana a madadin kwamishinan Ilimi, babban sakataren ma’aikatar, Bashir Baffa Ahmad, ya ce ma’aikatar ilimi zata ci gaba da baiwa hukumar goyon baya da haɗin kai domin cimma nasara.
A nasa jawabin daya daga cikin masu bayar da horo yayin taron, Dakta Auwal Halilu ya ce akwai bukatar ma’aikatan hukumar su san cewa kowane mutum zai iya neman wani ilimi ko darasi daga gurinsu.
Ya kuma bukace su da su mayar da hankali wajen adana bayanai wanda hakan zai taimaka wajen cigaban ilimi a jihar nan.
