Saurari premier Radio
21.8 C
Kano
Saturday, March 2, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKiwon LafiyaYadda fashewar slap a gadar Gadon Kaya ke haddasa hadura

Yadda fashewar slap a gadar Gadon Kaya ke haddasa hadura

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Masu ababen hawa a Kano na kokawa kan yadda fashewar slap a karkashin gadar kasa ta Gadon Kaya ke haddasa hatsari da asarar dukiyoyinsu.

 PREMIER RADIO ta ruwaito cewa wasu daga cikin slap din da aka shimfida a magudanar ruwan karkashin gadar sun farfashe, lamarin da ke janyowa wadanda basu san da matsalarba a sara mai yawa.

A cewar wani Malam Badamasi a karan farko da ya fada cikin ramin sai da ya fasa tayarsa sabuwa fil.

“lokacin da na fada cikin ramin sai da na fasa tayata sabuwa fil, kuma kowa yawasan yadda sabuwar taya ta ke da tsada yanzu.

Shima wani mai mota da ya nemi a sakaye sunansa ya ce abin ba a cewa komai da irin barnanar da wurin ke haifarwa.

Ya kuma roki dukka masu ruwa da tsaki da su duba al’amirn su taimaka su kai dauki karkashin gadar domin ceto rayuwar al’umma

“ina rokon gwamnatin Kano da su kai daukin gaggawa zuwa karkashin gadar, domin kubutar da jama’a.

Latest stories

CBN Ya Kwace Lasisin Yan Canji Sama da Dubu Hudu A Faɗin Nijeriya

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da soke lasisin...

Dangote ya bayar da shawarar mayar da kasuwar waya ta Farm Center zuwa cibiyar fasaha

Fitaccen attajirin nan, Alhaji Aliko Dangote, ya shawarci jami'ar...

Related stories

Yan Najeriya miliyan 60 suna fama da matsalar kwakwalwa

A yau ne ake bikin ranar lafiyar kwakwalwa ta...