Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya, NLC, ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta rage farashin man fetur, ta fara biyan tallafin albashi ga ma’aikata, tare da buɗe tattaunawa kan sabon mafi ƙarancin albashi.
Shugaban NLC, Joe Ajaero, ne ya bayyana buƙatun cikin saƙon ƙungiyar na bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kan Najeriya.
Ƙungiyar ta ce hauhawar farashin sufuri, abinci, haya da kuɗin makaranta na ƙara jefa ma’aikata da sauran ’yan Najeriya cikin matsin tattalin arziki.
NLC ta kuma bayyana cewa mafi ƙarancin albashin naira dubu 70 da ake biya a halin yanzu ya rasa ƙimarsa sakamakon hauhawar farashin kayayyaki, inda ta buƙaci kafa kwamitin da zai tsara sabon albashi kafin ƙarshen shekarar nan, domin aiwatar da shi a shekarar 2027.
Haka kuma, ƙungiyar ta yi kira da a rage kuɗin tafiyar da gwamnati, a ƙara bayyana yadda ake kashe kuɗaɗen gwamnati, tare da ƙara zuba jari a fannin ilimi, lafiya da ababen more rayuwa.
