Iran ta kai hari kan matatar Man fetur na Aramco na kamfanin Saudiya da jirgi maras matuki a hare-haren ramuwar gayya da ta ke kai wa a fadin kasashen yankin Gulf.
Iran ta kai harin ne a ranar Litinin, a cewar rahotanni.
Harin martani ne ga harin da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito daga majiyar masana’antu.
Matatar da ke Ras Tanura, na daya daga cikin matatun Saudi Arabiya da ke tace kusan gangar danyen mai 550,000 a kowace rana.
“Gobara ta tashi a matatar a bangaren da aka kai harin, wanda tarkacen jirage marasa matuki guda biyu da aka kakkabo suka haddasa yayin da suke kokarin kai hari kan ginin”. In Ji Kamfanin dillancin labarai na Saudi Press Agency.
Wanda hakan ya sa dakatar da aiki domin tantance barnar da harin ya haddasa yayin da matatar ke sauya salon ayyukanta.
Matatar Ras Tanura na daya daga cikin manyan matatun mai a duniya.
Iran ta harba makamai masu linzami da dama kan sansanonin Amurka da ke kasashen yankin Gulf, ciki har da Saudiya, bayan da Amurka da Isra’ila suka kaddamar da munanan hare-haren sama kan Iran, wadanda suka yi sanadiyyar kisan jagoran kasar, Ayatollah Ali Khamenei, da wasu jami’an gwamnatinsa.
Wani rahoto daga jaridar Washington Post a ranar Lahadi ya yi zargin cewa Yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman ne ya nemi Trump a asirce da ya kai wa Iran hari, yayin da a fakaice yake kiran a bi hanyar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu.
