Wata mata mai suna Oluwasola Victoria Adebayo ta rasu a wani yanayi mai tayar da hankali yayin da take jiran ‘yarta da ke rubuta jarabawar shiga jami’a (UTME) a jihar Ondo
Lamarin ya faru ne a mahadar Ilara-Mokin da ke karamar hukumar Ifedore, inda marigayiyar ta raka ‘yarta zuwa cibiyar rubuta jarabawar JAMB.
Shaidun gani da ido sun ce bayan sun isa wurin, matar ta koka da rashin lafiya kafin daga bisani ta fadi kasa.
“Ta ce ba ta jin dadi, sai kuma ta fadi,” in ji wani shaida. “Mutane sun yi kokarin taimaka mata amma ba ta farfado ba.”
An ce mutanen da ke wurin sun yi yunkurin farfado da ita, amma daga bisani aka tabbatar da rasuwarta a nan take.
A lokacin da lamarin ya faru, ‘yarta na cikin dakin jarrabawa, ba tare da sanin abin da ke faruwa ba.
Mai magana da yawun ‘yan sanda a jihar, DSP Abayomi Jimoh, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an bi dukkan matakan da suka dace kafin a mika gawar ga dan marigayiyar bayan binciken farko.
Lamarin ya jawo alhini a tsakanin mazauna yankin, inda ake nuna damuwa kan yadda irin wadannan lamura ke faruwa ba tare da gargadi ba.
