Kasashen Spain, Slovenia da Ireland sun bukaci kungiyar tarayyar turai EU da ta tattauna yiwuwar dakatar da yarjejeniyar hadin gwiwa da Isra’ila, suna mai cewa kungiyar ba za ta ci gaba da zama “a gefe” ba yayin da halin da ake ciki ke kara tabarbarewa a Gaza, yammacin Kogin Jordan da kuma Lebanon.
Ministan harkokin wajen Spain, Jose Manuel Albares, ya bayyana hakan kafin taron ministocin harkokin wajen EU da aka gudanar a Luxembourg, inda ya ce kasashen uku sun nemi a saka batun cikin ajandar taron.
“Spain tare da Slovenia da Ireland sun bukaci a tattauna dakatar da yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin EU da Isra’ila,” in ji shi. “Ina sa ran dukkan kasashen Turai za su mutunta abin da Kotun Duniya da Majalisar Dinkin Duniya ke cewa dangane da kare hakkin dan Adam.”
A wata wasika da suka aikawa shugabar harkokin wajen EU, Kaja Kallas, kasashen sun zargi Isra’ila da daukar matakan da suka saba wa dokokin kasa da kasa da kuma tauye hakkin bil’adama.
Sun ce matakan sun sabawa yarjejeniyar shekarar 1995 da ke tsara dangantakar siyasa, tattalin arziki da kasuwanci tsakanin bangarorin biyu.
Kasashen uku sun kuma nuna damuwa kan wani kudirin dokar Isra’ila da zai sanya hukuncin kisa ta hanyar rataya ga Falasdinawa, suna mai cewa hakan “babban take hakkin dan Adam ne.”
Bugu da kari, sun jaddada cewa halin da ake ciki a Gaza ya zama “mai tsanani sosai”, inda suka ce ana ci gaba da karya yarjejeniyar tsagaita wuta tare da karancin kayan agaji.
Sun kuma ce tashin hankali a Yammacin Kogin Jordan na karuwa, inda suka zargi ‘yan share wuri zauna da aikata hare-hare ba tare da hukunci ba, tare da hare-haren soji da ke janyo asarar rayukan fararen hula.
“kungiyar tarayyar turai ba za ta iya ci gaba da zama yar kallo ba,” in ji ministocin, suna kira da a dauki “matakai masu karfi da gaggawa.”
A wani bangare, Ireland na kokarin farfado da kudirin dokarta na hana kasuwanci da kayayyakin da ake samarwa daga matsugunan da Isra’ila ta mamaye a yankunan Falasdinawa.
Haka kuma, Spain da Slovenia sun riga sun dauki matakan takaita shigo da kayayyaki daga irin wadannan yankuna.
Kasashen uku sun kuma amince da kafa kasar Falasdinu a hukumance a watan Mayun 2024, matakin da ake ganin wani kokari ne na kara matsin lamba domin samar da mafita ta kasashe biyu.
