
Tsohon Gwamnan Jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau Ya Jagoranci Shugabanni Jam’iyyar PDP Zuwa Ta’aziyyar ‘yan wasan jihar da suka rasu
Ibrahim Shekarau ya jagoranci shugabanni da iyayen jam’iyyar PDP na Kano ne zuwa gidan gwamnatin jihar domin ta’aziyyar ga na mataimakin gwamnan Kwamared Aminu Abdussalam a gidan gwamnatin jihar.
A jawabinsa yayin ziyarar, Malam Shekarau ya ce, suna mika sakon ta’aziyyar su ne ga gwamnatin Kano da kuma iyalan wadanda suka rasu ne tare da yaba wa gwamnati bisa yadda ta nuna alhini da juyayi kan lamarin.
Mataimakin gwamnan jihar Kano kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya nuna jin dadinsa da ziyarar da tsohon gwamnan ya jagoranta domin jajantawa gwamnati da al’ummar Kano.
A yayin ziyarar Sardaunan Kano Malam Ibrahim Shekarau ya samu rakiyar shugaban jam’iyyar PDP na kano Yusuf Ado Kibiya da shugabannin shiyya na Kano ta tsakiya na jam’iyyar da kuma Shugabannin jam’iyyar na kananan hukumomi 15 da sauran manyan ‘ya’yan jam’iyyar.