Tsohon mataimakin shugaban ƙasa ya caccaki gwamnatin Bola Ahmed Tinubu kan matsalar rashin tsaro da ke ƙara ta’azzara a Najeriya, inda ya bayyana cewa shugabanci a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu ya durƙushe gaba ɗaya.
Atiku Abubakar ya yi wannan furuci ne bayan sace ɗalibai da malamai a garin Ogbomoso da ke jihar Oyo, tare da kashe wasu mazauna jihar Katsina da aka yi kwanan nan.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Atiku ya ce hare-haren da ake kai wa makarantu da al’umma a sassan ƙasar nan na nuna cewa mahukunta sun gaza wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Ya ce a duk lokacin da aka kashe mutane ko aka sace su, abin da gwamnati ke yi shi ne fitar da sanarwar ta’aziyya tare da alƙawarin hukunta masu laifi, amma daga baya komai ya mutu.
Atiku ya ƙara da cewa ‘yan bindiga da masu aikata ta’addanci sun fara aiki babu tsoro saboda sun fahimci cewa gwamnati ba ta da ƙarfin da za ta dakile su.
Ya kuma zargi shugaban ƙasar da yin magana ne kawai bayan an zubar da jini, yana mai cewa hakan ba shugabanci ba ne face gazawa.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya buƙaci gwamnatin tarayya ta ɗauki matakan gaggawa da za su kawo ƙarshen kashe-kashe da sace-sacen mutane da ke ci gaba da addabar Najeriya.
